Om Ya na Gani, Ya Sani, Ya na Kula
Ko kin täa jin kamar ba mai ganin ki? Ko kin täa jin kamar ba wanda ya san menene ke tafiye da ke ko ya damu da ke? Muna so a gan mu, a kula da mu, kuma a san mu, amma wassu lokuta bamu san inda zamu juwa ba. Rayuwa na cike da damuwowi da dama kuma wataran sai mu kan rasa abin yi sai mu ji ba mu da kowa.
"Don ¿an Mutum ya zo ne musamman garin neman abin da ya ¿ata, y¿ cece shi kuma." - Luka 19:10
Duk abin da mu ke ji, Mu na da Allah da ke ganin mu, wanda Ya san mu, wanda Ya na kula da mu. Ya aiko da ¿an Shi domin Ya nemo mu a duk inda mu ke, domin Ya lura da a lokacin da mu fäa ciki, kuma Ya san muräin zuciyar mu. Yesu Ya ba da ran Shi domin mu san Shi kuma mu samu rai na har abada da Shi.
A cikin Bisharan Luka, za mu labarin rayuwan Yesu. Luka ya nuna mana girman yadda Yesu Ya na gani, Ya sani, Ya na kuma kula da mutanen Shi. Yesu so da dama Ya kan yi duk abin da zai iya domin Ya taimake masu bukata kuma Ya nemo ¿atattu. Wannan bisharan ya nuna mana menene ainihin ma'anar bin Yesu da kuma abin da za mu biya domin mu bi Shi.
Ya na Gani, Ya Sani, Ya na Kula: Bisharan Luka binciken Littafi mai Tsarki ne na tsawon mako shida wadda aka shirya domin ya taimake mu gane wanene Yesu, da yadda Ya ke lura da mutanen Shi, da kuma yaya bin Shi ya ke. A cikin wannan binciken, za mu gan yadda za mu san Yesu mu kuma sa bangaskiyan mu a cikin Shi, ko da wani yanayi ne mu ka samu kan mu.
Mu häa kai tare cikin wannan binciken da littafi, ko ta yanan gizi, ko kan app na Love GOD Greatly. Za ki samu abubuwan da su ka shafi Ya na Gani, Ya Sani, Ya na Kula da rubuce rubuce da kuma jama'a , yayinda mu ke tafiya cikin wannan Bisharan Luka kuma mu na kara matso kusa da Mai Ceton mu mai gani, Ya sani, kuma Ya na kula.
Vis mer